1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin rufe bakin 'yan fafutika a Najeriya

September 28, 2016

A cewar rahoton da Kungiyar Amnesty ta fitar a ranar ta Laraba ta na da bayanai na jami'an tsaro sun tsare masu fafutikar Biafra, wasu sun bace baya ga wadanda suka rasu a hannun jami'an tsaro a Najeriya.

https://p.dw.com/p/2Qi29
Nigeria Proteste Chibok Mädchen
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta bayyana cewa Najeriya na kokari da barazana ta rufe baki da ma yin barazana ga 'yan jarida da masu zanga-zanga.

A cewar kungiyar wacce ke da ofishinta a birnin London cikin zanga-zangar da ta bayyana a baya-bayan nan akwai hana masu fafutika daga kungiyar nan mai kokari na ganin ansako 'yan matan Chibok sama da 200 da ke hannun Boko Haram, da hana 'yan Shi'a zanga-zangar a sako malaminsu bayan tsawon lokaci ya na hannun mahukunta da masu fafutikar samun 'yancin yankin Biafra a Kudu maso Gabashin na Najeriya.