1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin Musharraf da aikata babban laifi

November 17, 2013

Gwamnatin Pakistan ta yi imanin cewar tsohon shugaban mulkin soja Musharraf ya ci amanar kasa a shekara ta 2007. Saboda haka ta kudiri aniyar gurfanar da shi gaban kotu.

https://p.dw.com/p/1AJBR
Former Pakistani President Pervez Musharraf, speaks during a press conference in Karachi, Pakistan, Sunday, March 31, 2013. An angry lawyer threw a shoe at former President Pervez Musharraf as he headed to court in southern Pakistan on Friday to face legal charges following his return to the country after four years in self-imposed exile, police said. (AP Photo/Fareed Khan)
Hoto: picture-alliance/AP

Kasar Pakistan ta bayyana cewar za ta gurfanar da tsohon shugaban kasa Pervez Musharraf gaban kuliya bisa zarginsa da ta ke yi da cin amanar kasa. Ministan cikin gidan Chaudry Nisar Ali Khan ya nunar a birnin Islamabad cewa Musharraf ya kafa dokar ta baci a shekara ta 2007 a daidai lokacin da alkalai ke kalubalantar mulkinsa.

Wannan dai shi ne karon farko da aka zargi tsohon shugaban kasa da irin wannan laifi a Pakistan, duk da juye-juyen mulki da ta fi fama da su a shekarun baya. Idan ko an same Musharraf da wannan laifi, za a iya yanke wa tsohon shugaban na Pakistan hukunci rai da rai.

Wadanda suke nakalci kabli da ba'adi na harkokin siyasar wannan kasa suna ganin cewa gurfanar da Musharraf zai sake tayar da tsohon tsumi da ke tsakanin gwamnatin da ke ci a yanzu da kuma sojojin kasar. Idan za a iya tunawa Pervez Musharraf ne ya hambarar da gwamnatin firaminista na yanzu wato Nawaz Sharif a shekarar 1999. Sai dai Musharraf ya katse gudun hijira da ya ke yi domin ya samun damar tsayawa a zabukan gama gari da za su gudana a watan Mayu mai zuwa idan Allah ya kaimu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar