Zargin juyin mulki a kasar Malawi | Labarai | DW | 11.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zargin juyin mulki a kasar Malawi

Gwamnatin Malawi ta cafke wasu tsoffin ministoci bisa zargin yunkurin juyin mulki.

Rundunar 'yan sanda a kasar Malawi ta bayyana tsare wasu tsoffin ministocin kasar da kuma manyan jami'an gwamnati su 11 ciki kuwa harda dan uwan tsohon shugaban kasar bisa zargin yunkurin kifar da gwamnati, abinda kuma ya haddasa zanga zangar da ta sa jami'an 'yan sanda yin anfani da hayaki mai sa hawaye. Gungun mutanen dai ana zargin su ne da kokarin hana mataimakiyar shugaban kasa a wancan lokacin, wato Joyce Banda, darewa bisa kujerar shugabancin kasar a shekarar da ta gabata bayan mutuwar shugaba Bingu wa Mutharika. Daga cikin wadanda hukumomin suka tsare kuma harda Peter Mutharika, wanda ke zama ministan harkokin wajen kasar a karkashin shugabancin Bingu wa Muthawarika.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal