Zargin EU da takura masu neman mafaka | Labarai | DW | 17.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zargin EU da takura masu neman mafaka

Kungiyar Likitoci na Gari na Kowa, wato "Doctors Without Boders" ta sanar da cewa ba za ta sake karbar tallafi daga kungiyar Tarayyar Turai EU ba.

'Yan gudun hijira da ke son shiga Turai na cikin hadari

'Yan gudun hijira da ke son shiga Turai na cikin hadari

Janar sakatare na kungiyar Jerome Oberreit ne ya fadi hakan yayin wani taron manema labarai, inda ya ce kungiyar ta yanke wannan shawarar ne duba da yadda kasashen Turai ke kokarin ganin sun hana 'yan gudun hijira da bakin haure shiga kasashensu ko ta halin kaka. Oberreit ya kara da cewa:

"Mun yanke shawarar cewa kungiyar Likitoci na Gari na Kowa wato "Doctors Without Boders", za ta nisanta kanta daga duk wani tallafi da ya fito daga kasashen da ke goyon bayan tsarin neman mafakar da zai musgunawa rayuwar mutanen da ke cikin tsananin bukata, zan sanar da hakan ga dukkanin ofisoshinmu da ke fadin duniya."

Kungiyar dai ta zargi EU da rufe kan iyakokinta tare da mikaawa Turkiya ragamar kula da batun 'yan gudun hijirar da ke son tsallakawa zuwa Girka, tana mai cewa EU na neman zama mara tausayin dan Adam.