1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin cin zarafin yara a Afirka ta Tsakiya

Zainab Mohammed AbubakarFebruary 4, 2016

Hukumar kiyaye zaman lafiya ta MDD a kasar Afirka ta tsakiya da ke fama da rikici, ta sake sanar da sabon zargin cin zarafin yara mata a bangaren sojojinta.

https://p.dw.com/p/1Hq2W
Zentralafrikanische Republik UN Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Sabon zargin da ya kunshi cin zarafin kananan yara biyar, na zuwa ne kwanaki kalilan bayan bankado makamancinsa a bangaren dakarun Faransa da na Tarayyar Turai, wadanda ke amfani da yara, a wasu lokuta domin musayar abinci da kudi.

Kasar ta Janmhuriyar Afirka ta tsakiya dai na kokarin farfadowa daga rikicin addini da na kabilanci da ya barke bayan juyin mulki a shekarata 2013, wanda ya raba kan Musulmi da Kristocin kasar. Sai dai matsalar da kasar ke fuskanta a yanzu ita ce, cin zarafin yara mata da sojojin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa ke cigaba da yi, wadanda aka tura domin kare al'ummarta.

Sanarwar da ta fito daga hukumumar MDD ta MINUSCA da ke aikin kiyaye zaman lafiya a Afirka ta tsakiyar, na nuni da cewar an gano hakan ne bayan sakamakon binciken da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human rights Watch ta gudanar.