Zargin cin zarafin mata da yara a gidan yarin Maiduguri | Siyasa | DW | 26.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zargin cin zarafin mata da yara a gidan yarin Maiduguri

Gwamnatin Jihar Borno ta dauki matakin bincike kan wani rahoto wanda ya yi zargin cin zarafin mata da yara a gidan yarin Maiduguri ta hanyar yi masu fyade ko tilasta masu yin karuwanci da saka yara maza ayyukan luwadi.

Rahoton wanda wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta wallafa ya yi zargin cewa jami’ai a gidan yarin na hada baki da wasu masu zaman wakafi wajen cin zafarin mata da ‘yan mata da kuma maza da su ma ke zaman jarun. A cewa wannan rahoto akwai mata da ake tilasta musu yin karuwanci tare da yi wa yara mata fyade da tilasata yin luwadi da yara maza. Kuma in har kaddara ta sa matan sun dauki ciki ana tilasta musu zubar da shi abin da ke kara cutar da su.Wallafa wannan rahoto ya tayar da hankalin gwamnatin jihar da ta ce ya zo mata da ba zata, abin da ya sa ta kafa kwamitin bincike da zai gaggauta bincika wannan zargi tare da bankado masu hannu a wannan aika-aika domin fuskantar kuliya.

A cewar Alh Kashin Shetima Gwamnan Jihar Borno ba za su sa ido su kyale irin wannan abin kunya na faruwa, ba tare da daukar matakai da suka kamata ba na magance shi:

“Tarihi ya tabbatar da cewa gwamnatinmu ba ta sassauci ga duk wanda yake aikata laifuka dokokin kasa da kuma bata tarbiyar al’umma da ke shafar addini da al’adunmu. A wannan karon ma za mu tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi a wannan zargi da ake yi zai fuskanci fushin hukumomi kamar yadda doka ta tanadar”

Honnorable Kaka Shehu Lawal kwamishinan Shari’a na Jihar Borno wanda shi ne shugaban wannan kwamiti da gwamanti ta dora wa alhakin binciko wannan zargi, ya zayyana abubuwan da za su binciko tare da ba da tabbacin za su gaskiya wajen ayyukansu.

Tuni dai kungiyoyin fararen hula da kuma na kare hakkin Dan Adam suka nuna gamsuwa da wannan mataki da gwamnatin ta dauka tare yin kira ga kwamitin da ya yi aiki ba sani ba sabo.
Wasu 'yan Najeriyan sun nemi hukumomin su tsananta binciken matakin wasu kungiyoyin agaji da ake zargin sun kawar da kai daga wannan aika-aika domin a hukunta su tare da neman al’umma ta bai wa kwamitin hadin kai da ya kamata don gudanar da ayyukansa. 

 

Sauti da bidiyo akan labarin