Zargin cin hanci a Venezuela | Labarai | DW | 24.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zargin cin hanci a Venezuela

Tsofuwar alkalin alkalai ta kasar Venezuela wacce ta yi hijira zuwa Braziliya Luisa Ortega ta ce tana rike da bayyanai da dama da kuma hujjoji na cin hancin da karpar rashawa da Shugaba Nicolas Maduro yake yi.

Luisa Ortega  wacce ta isa Brazil  daga Kwalambiya ta sheda wa wani taro alkalai na kungiyar kasashen yankin Latine Amirka cewar  Nicolas Maduro  na hada baki da 'yan uwansa don satar kudi kasar. Ta kuma ce sun gano dalla biliyan 100 da sghuban ya sace,wani dan uwansa ya kai ya ajiye a Spain.