Zargin Amirka da leken asirin kasashen Turai | Labarai | DW | 21.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zargin Amirka da leken asirin kasashen Turai

Faransa ta bi sahun wasu kasashen Turai wajen bayyana kaduwarta bisa zargin cewar Amirka na mata leken asiri.

Fira ministan Faransa Jean-Marc Ayrault ya bayyana takaicinsa dangane da zarge zargen cewar Amirka na tatsar bayanai daga wayoyin tarho na al'ummar Faransa - a asirce, inda ya nemi hukumomi a birnin Washington, fadar gwamnatin Amirka su fayyace masa komi dangane da amsoshin da suka shafi batun.

Fira ministan na Faransa ya shaidawa manema labarai a birnin Copenhagen na kasar Denmark cewar, yayi matukar kaduwa da jin labarin cewar, wata kasar da Faransa ke abota da ita irin Amirka, za ta yi gaban kanta wajen satar bayanai - ta hanyar sadarwa daga daidaikun 'yan kasar, wanda ya ce ba tare da wata madogara ta tsaro ba, ko kuma wani ingantaccen dalilin yin hakan.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal