1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin almundaha a gasar FIFA na 2006

Abdullahi Tanko Bala
August 6, 2019

Ofishin babban mai gabatar da kara na kasar Switzerland ya zargi wasu tsoffin jami'an hukumar kwallon kafa ta Jamus da almundahana a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a 2006

https://p.dw.com/p/3NT5w
Fußball DFB-Funktionäre Horst R. Schmidt Theo Zwanziger Wolfgang Niersbach

An tuhumi Horst Rudolf Schmidt da Theo Zwanziger da kum a Wolfgang Niersbach tare da wani tsohon jami'in FIFA a Switzerland Urs Linsi da yiwa hukumar kwallon kafar Jamus rufa-rufa da kuma yaudarar kwamitin shirya gasar cin kofin kwallon kafar ta duniya ta 2006 game da zahirin wasu kudade da aka biya na sama da euro biliyan shida da rabi.

An kasa tantance musababbin kudin wanda aka biya ga Mohamed Bin Hammam tsohon dan takara na shugabancin FIFA saboda takardar da aika wa hukumomin Qatar a watan Satumbar 2016 don samun bayani ba a amsa ta ba. An yi zargin cewa kudin toshiyar baki ce domin samun kuri'a don baiwa Jamus damar daukar nauyin gasar wasannin.

Dukkan mutanen hudu dai sun musanta zargin. Sai dai a nasa bangaren Franz Beckenbauer ba zai fuskanci tuhuma ba saboda rashin koshin lafiya.