1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zapatero ba zai gana da Kagame ba

July 16, 2010

Ban Ki-Moon ne dai ya shirya ganawar shugabannin biyu a Madrid

https://p.dw.com/p/ONg6
Ban Ki Moon tare da Firaminista Jose Luis Rodriguez ZapateroHoto: AP

Firaministan Spain Jose Luis Rodriguez Zapatero yayi watsi da batun ganawa da shugaban Rwanda Paul Kagame bisa zargin da akewa shugaban da hannu a harbo jirgin saman tsohon shugaban Rwanda wanda kuma ya haifar da kisan kiyashin Rwanda na mutane rabin miliyan.

Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon ne dai ya shirya ganawar shugabannin biyu da nufin tattauna batun taron rage talauci na ƙarni da MƊD za ta gudanar a watan Satumba.

A maimakon haka Zapatero ya tura ministansa na harkokin waje ne domin ganawa da shugaba Kagame. Matakin Firaministan na Spain ya zo ne a daidai lokacin da shi kansa babban Sakataren Majalisar ta Ɗinkin Duniya, yayi suka ga shugaban dangane da kisan da aka yiwa wani ɗan jarida kuma ɗan adawar ƙasar a kwanan nan.

A wata ganawa da yayi da shugaban na Rwanda Paul Kagame a birnin Madrid, Ban Ki-Moon yayi kiran gudanar da cikakken bincike game da kisan gillar.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Mohammad Nasiru Awal