Zanga Zangar yin Allah wadai da Israela a Iran | Labarai | DW | 04.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga Zangar yin Allah wadai da Israela a Iran

Rahotanni daga Iran sun shaidar da cewa wasu mutane ku san dari,

sun kai hari kann ofishin jakadancin kasar Biritaniya dake kasar.

Hakan ya faru ne a cewar rahotanni, bisa irin goyon bayan da kasar take bawa kasar Israela, a game da yadda take kai hare hare a kasar Lebanon.

Kafafen yada labaru sun rawaito cewa, mutanen sun kai harin ne ta hanyar jefa duwatsu izuwa ofishin jakadancin na Biritaniya.

A lokacin zanga zangar, mutanen sun daddaga tutocin kungiyyar Hizbullah tare da fadar muna nan maganganu akan kasar Israela da kuma kasashen dake dafa mata baya.