1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar 'yan adawa a Kongo

September 27, 2014

Fiye da mutane dubu biyu ne suka gudanar da wata zanga-zanga a wannan Asabar din a birnin Kinshasa na Jamhuriyar dimokradiyar Kongo

https://p.dw.com/p/1DM0v
Hoto: AP

Masu zanga-zangar dai, na nuna adawarsu ga yunkurin shugaban kasar Joseph Kabila na sauya kundin tsarin mulkin kasar don ya samu sake tsayawa takara. Jam'iyyu da dama ne dai na adawa suka yi kira da a gudanar da wannan zanga-zanga, inda cikin su har da Vital Kamerhe tsohon shugaban Majalisar dokokin kasar, kuma shugaban Jam'iyyar "Union pour la Nation congolaise" UNC, da Bruno Mavungu Sakatare Janar na Jam'iyyar UDPS wadanda su ne shikashikan jam'iyyun adawa a wannan kasa, da kuma sauran shugabannin kananan jam'iyu daban-daban masu adawa da wannan mataki. 'yan adawar kasar ta Kongo dai na zargin Shugaba kabila dake mulki tun 2001 a wannan kasa, da neman sake makalewa kan karagar mulkin kasar duk kuwa da cewa ya kawo karshen wa'adin mulkin sa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba