1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar 'Yan adawa a Kenya

Abdourahamane HassaneJune 6, 2016

'Yan adawar na neman gwamnati ne da ta rusa hukumar zaɓen ƙasar wacce suke zargin cewar ba za ta iya shirya sahihan zaɓuka ba a shekara ta 2017.

https://p.dw.com/p/1J1Vk
Kenia Studenten Demo in Nairobi
Hoto: Reuters/T. Mukoya

Dubban jama'a a ne a Kenya suka gudanar da zanga-zanga a birnin Nairobi da kuma wasu sauran biranen ƙasar a ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar 'yan adawa wacce ta buƙaci gwamnatin da ta rusa hukumar zaɓen ƙasar saboda zarginta da nuna fifiko ga ɓangaran gwamnatin.'Yan sandan dai sun yi amfani da kulake da kuma barkono tsohuwa wajen tarwatsa masu boren wanda aka samu asara rayuka

An kashe mutum daya kana wasu da dama suka jikkata

Wasu dubban jama'ar ke nan da ke raira kalamun sukar gwamnatin a sa'ilin zanga-zangar wacce 'yan sanda suka kashe mutum ɗaya kana aka jikkata wasu shida a garin Kisumu da ke a yammacin Kenya a lokacin da 'yan sandar suka sha arangama da masu yin gangamin waɗanda suka tarwatsa da kulake da kuma barkono.To sai dai da yake mayar da martani sepeto janar na 'yan sandar kenya Joseph Boinet ya ce sun tarwatsa zanga-zangar ne saboda haramtacciya ce.

Kenia Leiche von Demonstrant in Proteste gegen die Wahlkommission (IEBC)
Hoto: Reuters/M. Eshiwani

"Kotu ta gargaɗi duk ƙungiyoyin da ke da niyar shirya-shirya zanga-zanga da su fara neman izini daga hukumomi tukuna. "

An gaza cimma sulhu tsakanin gwamnatin da 'yan adawar a kan IEBC

Tun a cikin watan Afrilun da ya gabata 'yan adawa da ƙungiyoyin farar hula ke gudanar da zanga-zanga domin tilasta wa gwamnatin ta Kenya da ta rusa hukumar zaɓen ta IEBC wacce suke zargin cewar ba za ta iya shirya sahihan zaɓuka ba da aka shirya gudanarwa a cikin watan Augusta na shekara ta 2017 a ciki har' da na shugaban ƙasa.Wanda za a sake fafatawa tsakanin shugaba Uhuru Kenyatta mai shekaru 54 da kuma jagoran 'yan adawa na ƙasar Raila Odinga ɗan shekaru 71 da haifuwa.A cikin watan Mayu da ya gabata mutane uku aka kashe a zanga-zangar da aka yi a yammacin ƙasar ta Kenya wanɗanda 'yan sanda suka harbe har lahira abin da ya janyo martani da ƙugiyoyin kare hakin bil Adama

Kenia Nairobi Demonstration Opposition
Hoto: DW/A. Kiti