1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar nuna goyon baya ga dakarun Nijar

Larwana Malam HamiFebruary 17, 2015

Duk da cewa 'yan adawa ba su je gangamin ba, matan sojoji da sarakunan gargajiya sun hallara dan nuna takaicinsu dangane da yanayin da al'umma kan shiga idan wani abu ya faru da dakarun

https://p.dw.com/p/1EdRl
Niger - Demonstration gegen den Terror in Zinder
Hoto: DW/L. Hami

A yayin da gwamnatin jamhuriyar Nijar ta kirayi 'yan kasar a zanga-zangar gama gari a fadin kasar don nuna goyon baya ga sojojin kasar a yakin da suke yi da Boko Haram, a Damagaram cibiyar 'yan adawa kiran ya samu karbuwa duk da tuwon fashin da 'yan adawar suka ci game da halartar jerin gwanon da ya wakana cikin lumana.

Cikin irin rera wannan take da bada kwarin gwiwa ga dakarun kasar ne dai zanga-zangar ta gudana a nan Damagaram wadda ta faro tun daga dandalin juyayi na dalibai har zuwa fadar gwamnatin Jaha Mai Daji Alambay ne da kuma kusoshin gwamnati uka karbi yan zanga zangar Inda a karshe ya jinjina masu Damtse

Talakawa sun yi farin cikin samun wannan dama

Tarin motocin sufuri da kuma masu zaman kansu ne shake da mutane suka kwararo zuwa Birnin a matakin farko na fidda jakki daga duman sarakuwa. Jama'ar da suka halarci wannan jerin gwano dai sun bayyana ra'ayoyin su.

Niger - Demonstration gegen den Terror in Zinder
Hoto: DW/L. Hami

A dai binciken da na gudanar matakin da 'yan adawa suka dauka na kin halartar jerin gwanon sun cika shi ba a nan Damagaram ba hatta birnin Diffa inda rikicin ke wakana 'yan adawa basu halarci taron gangamin da al'ummar suka yi ba ko da yake a Diffa gidauniyar da aka buda domin taimakawa iyallan sojojin da suka rasu ce ta cika makil har ta batse, an kuma rufe zanga zangar da adu'o'in samun nasara a yakin daake ciki.