1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Neman dakile matsalar tsaro

December 14, 2021

Kungiyoyin fararen hula a jihar Katsina, sun gudanar da zanga-zangar lumana domin ci gaba da nuna damuwarsu kan kashe-kashen al'umma a arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/44GD9
Nigeria Abuja | Proteste | Entführte Studenten
Al'ummar arewacin Najeriya, na bukatar a kawo karshen matsalar tsaro a yankinHoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Kungiyoyin dai sun gudanar da zanga-zangar ne a cikin birnin Katsina, inda suka rinka furta kalaman kyama a kan yadda ake ci gaba da halaka mutane ba gaira ba dalili. Suma kungiyoyin mata ba a barsu a baya ba, wajen nuna taikaicinsu kan abin da ke faruwa na rashin tsaron a arewacin Najeriya wanda hakan yasa suka bi ayarin zanga-zangar. A cewar Dakta Yahuza Ahmed Getso masanin tsaro a Najeriya, zanga-zangar na isar da gagarumun sako ga mahukunta. Al'umma dai na ci gaba da nuna fushinsu a jihohin arewacin Najeriyar har ma da Abuja babban birnin kasar, sakamakon yadda 'yan bindiga ke cin karaensu babu babbaka wajen kashe mutane suna mayar da mata zawara su kuma mayar da yara marayu marasa galihu.