Zanga-zangar janye tallafin mai a Sudan | Labarai | DW | 26.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar janye tallafin mai a Sudan

Kwanaki hudu 'yan Sudan suka shafe a jere suna tayar da kayar baya da nufin nuna bancin ransu kan janye tallafin man fetur da gwamnati ta yi.

'Yan Sudan na shirin sake fantsama kan titunan kasar a wannan Alhamis domin ci-gaba da zanga-zangar nuna adawa da janye tallafin man fetur da gwamntin ta yi. Akalla mutane shida ne dai suka rasa rayukansu a ranar Laraba a babban birnin kasar Khartum da kuma Omdurman, bayan da 'yan sanda suka yi amfani da barkono mai sa hawaye da kuma kulake wajen tarwatsa masu zanga-zanga.

Ma'abota sabbin hanyoyin sadarwa na zamani sun bayyana cewa gwamnati ta katse shafukan Facebook da kuma Twitter domin hana yada zahirin abin da ke faruwa a kasar. Sai dai har ya zuwa yanzu ba a tantance sahihancin wannan zargi ba. Gwamnatin kasar ta Sudan ta sanar da rufe makarantu har yazuwa karshen wannan wata, bayan da masu gangamin suka yi ta cunna wa manyan gine-ginen gwamnati wuta tare da datse hanyoyi da shingaye.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal