Zanga-zangar Hong Kong ta dauki sabon salo | Labarai | DW | 01.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar Hong Kong ta dauki sabon salo

Masu zanga-zanga na Hong Kong sun yi barazanar mamaye gine-ginen gwamnati

Shugaban daliban da ke zanga-zangar kan bunkasa demokaradiya a tsibirin Hong Kong, ya yi barazanar cewa za su mamaye mahimman gine-ginen gwamnati, muddun jagoran tsibiri bai ajiye madafun iko ba.

Wannan sanarwa ta zo bayan kwashe kwanaki hudu ana zanga-zangar.

Tuni tsibirin Taiwan ya goyi bayan masu zanga-zangar. Taiwan yana cikin yankunan da China ke sha'awar komawa karhse tsarin kasar, kamar yadda aka yi wa tsibirin ha Hong Kong.

Mahukuntan na Taiwan sun bukaci China ta cika alkawarin da ta dauka na sakin mara wa 'yan Hong Kong bisa yarjejeniyar da ta kulla da Birtaniya, wadda ta janyo aka sake mayar da tsibirin karkashin ikonta a shekarar 1997. A cikin wata sanarwa Shugaba Taiwan Ma Ying-jeou ya ce muddun China ta amince 'yan Hong Kong su kada kuri'ar wanda zai mulkin tsibiri, haka zai yi matukar cike sabanin da ke tsakanin sassan biyu na Taiwan da china.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu