Zanga-zangar goyon bayan jami′an tsaro a Nijar | Labarai | DW | 09.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar goyon bayan jami'an tsaro a Nijar

Daruruwan mutane ne suka yi zanga-zanga ta lumana a wannan Asabar din a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar, da ma wasu manyan biranen kasar kan yakin da ake da Boko Haram.

Protest gegen Boko Haram in Niamey, Niger

Masu zanga-zangar adawa da Boko Haram a Nijar

Masu zanga-zangar dai a birnin Yamai, Tahoua, da Damagaram, sun yi ta rera kalammai na nuna adawa ga Boko Haram, da kuma na goyon baya ga jami'an tsaron kasar, inda a birnin na Yamai suka yi jerin gwano kafin daga bisani su tare a harabar majalisar dokokin kasar inda suka gudanar da taron gangami.

Kungiyoyinn fararan hulla ne dai, gami da na kwadago, da kungiyoyin dalibai, suka shirya wannan zanga-zanga wadda ita ce ta biyu da aka shirya a kasar tun bayan da sojojin na Nijar suka tsunduma a cikin yaki da Boko Haram. A farkon watan Yuni ne dai da ya gabata, mayakan na Boko Haram suka hallaka sojojin na Nijar 26 tare da jikkata wasu da yawan gaske a garin Bosso da ke cikin jihar Diffa a Gabashin kasar.