1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar Ferguson ta dauki sabon salo

August 20, 2014

Mako guda bayan da wani dan sanda farar fata ya harbe saurayi bakar fata, Michael Brown a Ferguson a jihar Missouri a Amirka, har yanzu kura bata lafa ba a tashin hankalin da ya biyo baya.

https://p.dw.com/p/1CyNr
USA Proteste in Ferguson 19.08.2014
Hoto: Getty Images

. Binciken kwararrun likitoci ya nuna cewar saurayin ya mutu ne bayan da dan sandan ya yi zargin cewar yana dauke da makamai, kuma ya zama barazana a gareshi. Duk da dokar hana fitan dare, amma ana ci gaba da samun tashin hankali tsakanin al'ummar Feguson, mafi yawansu bakar fata da 'yan sanda da jami'an tsaro.

Garin Ferguson mai yawan jama'a dubu 21, inda kashi biyu cikin kashi uku bakar fata ne, ya na da 'yan sanda gaba daya 53, inda daga cikinsu, guda 50 suka kasance farar fata. Tashin hankalin da ya biyo bayan kashe saurayi Michael Brown da dan sanda farar fata yayi, wata alama ace dake nunar da halin da al'ummar bakar fata suke ciki a wannan gari, inda ko da shike sune masu rinjaye, amma basu da ikon fadi aji, ko tsoma bakinsu a cikin yadda ake tafiyar da mulkinsu.

Wani masanin zamantakewa, Darnell Hunt, na cibiyar nazarin zaman bakar fatan Amirka a jami'ar California, ya yi zargin cewar garin Ferguson ya zama alamar koma bayan rayuwa zuwa shekaru na 40, wato zamanin da aka fara bullo da fafitikar neman 'yancin bakar fata a kasar baki daya. Hunt ya ce ya na da wuya a Amirka din mutum ya ji labarin inda 'yan sanda suka kashe wani farar fata da baya dauke da makami, saboda ra'ayinsa, bakar fata a idanun mafi yawan fararen Amirka, a duk inda yake barazana ce a garesu.

Antonino D. French / Ferguson / USA
Hoto: DW

Masu zanga-zanga a garin Ferguson, sun nemi a tsare dan sandan da ya harbe wannan saurayi, Michael Brown, wanda ya zuwa yanzu, dakatar da shi kawai aka yi daga aiki, yayin da ake ci gaba da bincike. Shugaban Amirka Barack Obama ya tura sakatarensa na shari'a zuwa garin, yayin da wata tawaga ta alkalai da jami'an hukumar leken asiri ta FBI suke tafiyar da bincike kan abin da ya faru a zahiri. A game da tashin hankalin da yaki ci kuma yaki cinyewa a garin, Obama yace:

"Yayin da nake iya fahimtar rashin jin dadi da bakin cikin da masu zanga-zangar suke ciki sakamakon mutuwar Micgael Brown, amma maida wannan fushi ya zuwa tashin hankali da dibar ganima da yawo da bindigogi, ko kuma kaiwa yan sanda hari, babu abin da zasu haifar ila kara haddasa rikici da jefa garin cikin rudami".

To sai dai yayin da ake ci gaba da binciken dalilai ko yadda aka kashe Brown, masu zanga-zangar basu yi imanin za'a dauki wani mataki kan dan sandan da ya aikata wannan kisa ba. Mazauna garin basu ma yarda da yan sanda baki daya ba. Hakan ya kai ga tambayar, idan jama'a basu yarda da yan sanda ba, to zasu kua aminceda jamki'an tsaron taraiya da aka tura su garin domin kwantar da kurar rikicin? Wani limamin kirista, Pastor Stoney Shaw yace:

Polizeigewalt in Ferguson 19.08.2014
Hoto: Getty Images

"Dukkaninmu a nan abin da muke son sani shine tsage gaskiya, mu san ainihin abin da ya faru. Daga nan kuma sai daukar matakai na hakika domin zartas da hukuncin da ya dace."

Ranar Talata aka kuma sami labarin cewar 'yan sanda sun sake harbe wani bakar fata a kusa da Ferguson, wanda suka ce yaki yarda a kama shi, duk da laifuka masu tarin yawa da ake zargin ya aikata. Ya zuwa yanzu dai "yan sandan da jami'an tsaro sun maida hankali ga amfani da gas mai sanya hawaye domin tarwatsa 'yan zanga-zanga da ci gaba da nuna rashin jin dadinsu sakamakon kashe Brown, duk da dokar hana fitar dare a garin na Ferguson.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Yusuf Bala

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani