1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dalibai na zanga-zanga a Indiya

Abdul-raheem Hassan
February 9, 2022

Zanga-zangar dalibai na dada daukar zafi a sassa dabam-dabam na kasar Indiya don nuna goyon bayansu ga dalibai mata musulmai da aka hana shiga aji da hijabi a kudancin jihar Karnataka da ke Kudu maso yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/46kic
Indiya, Karnataka
Hoto: Imtiyaz Khan/AA/picture alliance

Daruruwan daliban Indiyan sun cigaba da hawa kan titunan kasar dauke da kwalayen rubutu na tir da gwamnati, bayan da makarantu da dama suka hana dalibai shiga aji da hijabi bisa umarnin ma'aikatar ilimi. Matakin da ya kai ga rufe makarantu na tsawon kwanaki uku saboda zazzafar zanga-zangar da iyaye da dalibai suka yi. Muskan Khan, na cikin daliban da suka fito zanga-zanga, inda ta ce "Kowane addini yana da 'yanci, Indiya kasa ce mai hadin kai. Don haka kowane addini yana da 'yanci. Suna bin al'adun su kuma ni ina bin al'adata. Ya kamata su barmu mu bi al'adunmu kada mu kawo cikas."

Cikin fitattu da suka fito fili suna nuna goyoyn bayansu ga da daliban har da Malala Yousafzai, mai fafutuka kan ilimin 'yan mata wacce ta samu lambar yabo na zaman lafiya ta Nobel inda ta tambayi shugabannin Indiya a cikin wani sakon twita cewa " a dakatar da mayar da mata musulmi saniyar ware"

Sai dai a gefe guda an samu dalibai mabiya addinin Hindu, da su ma suka fito zanga-zangar nuna goyoyn bayan su ga matakin hukumar ilimi na hana mata musulmai shiga aji da hijabi.  

Gwamnatin jihar Karnataka, inda adadin yawan musulmi kashi 12 cikin 100 ne kacal, kuma jam'iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) mai kishin addinin Hindu ta Firaiministan Indiya Narendra Modi ta ce wajibi dalibai su bi ka'idojin sutura da makarantu suka gindaya.

Jam'iyyun adawa da masu suka suna zargin gwamnatin BJP a matakin tarayya da jiha na nuna wariya ga tsirarun al'ummar Musulmi. Amma Firaminista Modi ya kare matakin da cewa manufofin sa na tattalin arziki da zamantakewa suna amfanar duk Indiyawa.