1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawar Kwango ta ci tura

Mouhamadou Awal Balarabe
December 19, 2017

'Yan adawan Kwango sun shirya zanga-zanga don yi tir ga aniyar Kabila na ci gaba da shugabanci shekara guda bayan karewar wa'adinsa. Sai dai mutane kalilan ne suka fito.

https://p.dw.com/p/2pfhf
Kongo Opposition
Hoto: picture alliance/dpa/AP Photo/J. Bompengo

'Yan adawan Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango sun nuna bakin cikinsu dangane da rashin samun karbuwa da zanga-zangar da suka shirya bai yi ba sakamakon haramtata da hukumomi suka yi. Da ma dai sun so yin amfani da cikan shekara guda da karewar wa'adin mulkin shugaba Joseph kabila a hukumance wajen neman a gaggauta yin zaben don raba kasarsu da mulkin da suka danganta na sai madi ka ture.

Cikin wani faifai bidiyo Joseph Tshisekedi da ga marigayi madugun 'yan adawan Kwango ya ce ruwan sama da rarrbuwar kawuna da aka samu a bangaren adawa ne ummal aba'isan rashin samun wannan nasara. Dama dai gwamnan Kinshasa ya gargadi 'yan kasar da su guji gudanar da zanga-zanga adawa idan suna son kansu da lafiya, saboda an rigaya a tsayar da jadawalin zaben shugaban kasa zuwa 23 watan disemban 2018.