Zanga-zangar adawa da mulki Kabila | Labarai | DW | 24.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar adawa da mulki Kabila

Masu adawa da cigaba da zaman Joseph Kabila na Jamhuriyar Demokradiyar Kwango a kujerar shugaban kasa da ke samun goyon bayan cocin Katolika na kasar za su yi zanga-zanga a gobe don matsa masa kan ya sauka daga mulki.

Kungiyar nan ta Lay Coordination Comittee (CLC) ce ta kira wannan zanga-zanga ta ranar Lahadi inda al'ummar kasar za su bazama kan tituna neman Kabila ya bar mulki. Gabannin fara wannan zanga-zanga, mabiya darikar Katolika da dama kasar sun gudanar da addu'o'i na musamman a jiya Juma'a, inda wasu daga cikin limaman cocin Katolikar kasa suka bukaci mabiya addinin Kirista da su shiga a dama da su a zanga-zangar wadda suka ce ta lumana ce.