1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da hukuncin kisa a New York

Yusuf BalaDecember 4, 2014

Kisan bakar fata dai a wanke 'yan sanda farar fata abu ne da ke neman zama ruwan dare a Amirka. Lamarin kuma da ke neman jefa Amirka cikin tsaka mai wuya.

https://p.dw.com/p/1Dz43
New York USA Proteste 4.12. Eric Garner
Hoto: Reuters/Eric Thayer

Daruruwan masu zanga-zanga sun fantsama a tituna da dama a birnin New York, bayan da alkali mai sauraren kara ya gaza cajin wani dan sanda farar fata da ya shake wani mutum bakar fata, shakar kuma da ta yi sanadin mutuwar mutumin. Wannan kuwa na zuwa ne kwanaki kadan bayan da irin wannan hukunci ya haifar da mummunar zanga-zanga a wasu biranen Amirkar.

Ba da dadewa bane bayan bayyanar wannan hukunci, masu zanga-zagar suka bayyana a cibiyar Rockefeller da ke a birnin na New York, inda suke wakoki irin na nuna adawa da hukuncin da suka hadar da cewa "Idan babu adalci ba zaman lafiya" wannan hukunci dai na zama wani fami kan hukuncin da aka yanke a shari'ar dan sanda farar fata da ya kashe Micheal Brown bakar fata da baya dauke da makami.

A cewar Bill Bratton kwamishinan 'yan sanda a birnin na New York, ya zuwa yanzu sama da masu zanga-zanga talatin ne aka kame a wannan zanga-zanga da ke ci gaba da gawurta.