Zanga-zangar adawa a Zimbabuwe | Labarai | DW | 17.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar adawa a Zimbabuwe

'Yan sandan Zimbabuwe sun harba hayaki mai sa hawaye da ruwa zafi domin tarwatsa masu zanga zanga da suka yi gangami a Harare.

Zanga-zangar adawa da gwamnatin ta zama ruwan dare a kasar ta kudancin Afirka game da abin da masu zangar-zangar suka ce sun kosa da yadda tattalin kasar ke ci gaba da tabarbarewa. Daya daga cikin masu zanga-zangar ya yi tsokaci yana mai cewar

Ya ce: 'sakon a bayyane yake dole ne a yanzu Robert Mugabe ya yi murabus ya ba da damar shata sabon babi ga kasar. Wannan shi ne abin da za mu ci gaba da yi ko ya saurara ko kuma bai yi ba."