Zanga-zangan ′yan sanda a Tunisiya | Labarai | DW | 25.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangan 'yan sanda a Tunisiya

'Yan a Tunisiya sun sake fitowa a wannan Alhamis din inda suka yi zanga-zanga domin neman karin albashi, inda suka ce ana nuna musu bambanci.

default

'Yan sanda na zanga-zanga a Tunisiya

Hukumar jami'an tsaron cikin gidan kasar ta Tunisiya ce dai ta kira wannan taron gangami bayan tattaunawa tsakanin bangarorin ta watse baram-baram. Sanye cikin kayayakin fararan hulla, 'yan sanda sun ce ana nuna musu bambanci, inda suke furta kalamman nuna kyama ga Firaministan kasar Habib Essid.

Mai magana da yawun 'yan sandan Chokri Hamada ya ce "suna bukatar albashi dai dai irin yadda ake bai wa hukumar sojoji, inda ya kara da cewar ba ta kamata ba suna aiyyuka guda amma ana fifita wasu wajen samun albashi. Tun dai yau da 'yan watanni ne 'yan sandan kasar na Tunisiya ke neman a kara musu albashi, amma hakar tasu ta kasa cimma ruwa.