An kafa dokar hana fita a Bagadaza
October 3, 2019Talla
'Yan sanda sun rika yin amfani da harsashen gaske wajen tarwatsa masu ganganmin a kwanaki uku jere, wadanda ke zargin 'yan siyasar da laifin cin hanci da kuma rashin aikin yi da ake fama da shi. A halin da ake ciki gwamnatin ta Iraki ta kafa dokar hana fita a birnin Bagadaza tare da dakatar da zirga-zirgar ababen hawa.