Zanga-zanga ta janyo rufe jami′a a Jos | Labarai | DW | 25.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga ta janyo rufe jami'a a Jos

Hukumar gudanarwa ta jami'ar Jos da ke jihar Pilato a Tarayyar Najeriya ta bada umurnin rufe jami'ar ba tare da wani bata lokaci ba.

default

Rufe jami'ar dai ya biyo bayan wata zanga-zangar da daliban jami'ar ke yi wadda a Talatar nan ta shiga yini na biyu sakamakon korafi da suka yi na karin kudin makaranta. Wakilinmu na Jos fadar gwamnatin jihar Plato, Abdullahi Maidawa Kurgwi, ya ruwaito cewa an jibge jami'an tsaro a kan titin Bauchi da ke Jos da sauran manyan tituna da ke shiga jami'ar ta Jos, inda aka bai wa dalibai umurnin barin gidajen kwanansu da kuma harabar jami'ar nan take. Mataimakin shugaban jami'ar Farfessa Hayward Mafuyai ya ce akwai kwamiti da aka kafa da zai tattauna da daliban domin jin koken nasu. Koda a wannan Talata din ma dai an yi fito na fito tsakanin daliban jami'ar ta Jos da kuma jami'an tsaron da aka tura don kwantar da hankula, inda wasu daliban suka yi kone-konen tayoyi a wuraren da suka yi zanga-zangar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal