Zanga-zanga na kara kamari a Ukraine | Labarai | DW | 02.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga na kara kamari a Ukraine

Al'ummar kasar Ukraine na ci gaba da yin zanga-zangar kin jinin gwamnati, duk kuwa da kokarin da jami'an tsaro ke yi na dakile su

Anyi artabu tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga dake nuna bacin ransu a kasar Ukraine dangane da kin sanya hannu kan yarjejeniya, da Firaministan kasar Viktor Yanukovich yayi da kungiyar hadin kan Turai.

Dubun-dubatar masu zanga-zanga ne dai suka yi wa birnin Kiev tsinke, domin nuna adawarsu da gwamnatin kasar, yayin da jami'an 'yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar da karfin tuwo.

Ana dai zargin kasar Rasha da hannu cikin kin sanya hannu kan yarjejeniyar zamowa mamba a kungiyar hadin kan Turan, da firaminista Yanukovich na Ukraine din yayi.

Mawallafiya Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Saleh Umar Saleh