Zanga-zanga kan cin zarafin mata a Köln | Labarai | DW | 09.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga kan cin zarafin mata a Köln

Jagoran fafutuka ta PEGIDA Lutz Bachmann ya sanya hotonsa a shafin Twitter inda yake cewa masu aikata fyade daga cikin 'yan gudun hijira ba a musu maraba a Jamus.

Deutschland Pegida

PEGIDA kungiya me adawa da yawaitar baki a Jamus

Har ya zuwa yanzu dai ana cikin hali na dari-dari a birnin Köln na nan Jamus sakamakon cin zarafin mata da aka samu wasu mutane da ake zargi sun fito daga kasashen Larabawa daga Arewacin Afirka da aikatawa a ranar jajiberin sabuwar shekara, Lamarin ya sanya kiran gangami na nuna kyamar wannan halayya a ranar Asabar din nan daga kungiyar nan da ta yi shuhura wajen nuna kyama ga yawaitar Musulmi a nan Jamus wato PEGIDA.

Da misalin karfe daya agogon GMT ne dai aka fara wannan gangami a birnin na Köln. Jagoran wannan fafutuka ta PEGIDA Lutz Bachmann ya sanya hotonsa a shafin Twitter inda yake cewa masu aikata fyade daga cikin 'yan gudun hijira ba a musu maraba a Jamus. Da dama dai irin wadannan 'yan fafutuka na nuna yatsa ga shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel wacce suke ganin tsarinta na barin baki sama da miliyan daya su shiga kasar shi ya jawo haka.

Sai dai ita ma shugabar ta bayyana cewa za a sake nazari kan dokar da ta shafi mayar da wadanda suka aikata laifi kasashensu na asali.