1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Greenland: Zanga-zanga za ta kwato 'yanci?

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 22, 2026

Sama da al'ummar Tsibirin Greenland 500 ne suka gudanar da zanga-zanga, a wani mataki na nuna adawa da yunkurin shugaban Amurka Donald Trump na kwace iko da tsibirin.

https://p.dw.com/p/5ECY9
Greenland | Nuuk | Zanga-zanga | Amurka | Donald Trump
Zanga-zangar adawa da matakin Donald Trump a Tsibirin GreenlandHoto: Tim Barsoe/REUTERS

Wannan na zuwa ne, bayan kaddamar da sabuwar harabar karamin ofishin jakadancin Amurka a Nuuk. Masu zanga-zangar sun yi ta rera taken adawa da Amurka da kuma daga kwalaye da aka rubuta "Tafi Gida Amurka" da "Ku Sa Amurka Ta Tafi" da kuma "Mu ba na sayarwa ba ne."

Greenland | Nuuk | Zanga-zanga | Amurka | Donald Trump
Har yanzu Tsibirin Greenland na fuskantar barazanar Donald TrumpHoto: Florent Vergnes/AFP

Trump ya sha nanata cewa, tilas Amurka ta kwace iko da Tsibirin Greenland saboda dalilai na tsaro. Ya kuma nunar da cewa, idan har bai karbe iko da tsibirin da ke da kwarya-kwaryar 'yanci daga Denmark ba to yana iya fadawa hannun Chaina ko Rasha da ke zaman abokan hamayyar kasarsa.