Zanga-zanga a Pakistan | Labarai | DW | 06.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a Pakistan

Dubun dubunan jama´a, a ƙasar Pakistan, su ka share daren iiya, su na gudanar da zanga-zangar lumana.

Jamar ƙasar na nuna goyan, ga shugaban kotin ƙoli Ifkhar Chaudry, da shugaba Pervez Musharaf ya sallama daga aiki, a watan Maris da ya wuce.

Rahottani daga birnin Lahore, cibiyar masu zanga-zangar, sun ce, wannan itace zanga-zanga mafi tsanani, da shugaban ya taɓa fuskanta, tun hawan sa kan karagar mulki a shekara ta 1999.

Al´ummar ƙasa ta yi kyakyawar shaida ga tsofan shugaban kotin ƙolin, ta kuma yi watsi da da abinda ta kira, mummunan hukunci, da Musharaf ya yanke masa,ba dan komai ba , pace cimma wani buri na siyasa.

Kazaliak kunguiyoyinkare hakkokin bani adama da na alkalai sun bada goyan baya ga zanga-zangar.

Sun kuma zargi shuga Pervez Musharaf, da yin karan tsaye, ga harakokin shari´a.