1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Masar

Sadissou YahouzaNovember 30, 2012

Dubban mutane ne a Masar su ka gudanar da zanga-zanga bayan da majalisar rubuta kundin tsarin mulkin ƙasar ta amince da daftarin kundin tsarin mulkin da aka rubuta.

https://p.dw.com/p/16twg
Anti-Mursi protesters chant anti-government and anti-Muslim Brotherhood slogans as they gather at Tahrir Square in Cairo November 27, 2012. Opponents of President Mohamed Mursi rallied in Cairo's Tahrir Square for a fifth day on Tuesday, stepping up calls to scrap a decree they say threatens Egypt with a new era of autocracy. REUTERS/Ahmed Jadallah (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Proteste in Kairo ÄgyptenHoto: Reuters

Masu zanga-zangar sun yi ta rera kalamai na ƙin jinin shugaba Muhammad Mursi da kuma kwatankwacin waƙe-waƙen da aka yi lokacin guguwar neman sauyin da ta kawar da shugaba Hosni Mubarak daga karagar mulki.

Masu zanga-zangar dai da ma jam'iyyun adawa gami da ƙungiyoyin Kiristoci da na musulmi masu sassaucin ra'ayi sun ce ba a dama da su ba yayin rubuta kundin tsarin mulkin wanda aka rubuta shi cikin ƙanƙanin lokaci.

Masu sanya idanu kan harkokin na Masar dai na cewar an yi hakan ne don su takawa kotuna Masar ɗin birki don kada su ɗau wani mataki na kalubalantar yunƙurin.

Nan gaba ne dai za a yi ƙuri'ar raba gardama kan daftarin tsarin mulkin bayan Shugaban ƙasa ya amince da shi.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Yahouza Sadissou Madobi