1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Burundi ta kazanta

Yusuf BalaMay 12, 2015

Ya zuwa yanzu dai 'yan sanda na amfani da harsashin gaske wajen tarwatsa masu zanga-zanga, abin da ke kara yawan adadin wadanda ke mutuwa.

https://p.dw.com/p/1FOky
Unruhen in Burundi
Masu zanga-zanga a BurundiHoto: picture-alliance/AP Photo/Delay

Zanga-zangar adawa da yunkurin gwamnatin shugaban kasar Burindi Pierre Nkurunziza a karo na uku na ci gaba da gawurta bayan da a ranar Talatan nan ma dai 'yan sanda suka halaka wani mai fafutika adaidai lokacin da dubban masu zanga-zanga ke gudanar da maci.

Kamar yadda wani da ya shaida lamarin ya bayyana, ya ga lokacin da 'yan sanda suka harbi daya daga cikinsu inda take ya ce ga garunku nan a lardin Buterere da ke zama wani yankin na birnin Bujumbura.

A yayin wannan zanga-zanga bayan wasu mutane da suka sami raunika, an banka wuta a wani gidan jami'in gwamnati da wasu motoci na gwamnati uku.

Yanayin na ci gaba da kazanta yayin da 'yan sanda ke amfani da harsashin gaske wajen tarwarsa masu zanga-zanga kamar yadda Pierre Claver Mbonimpa daga wata kungiya mai fafutikar kwato 'yancin al'umma ya nunar.