Zanga zanga a ƙasar Cyprus | Labarai | DW | 24.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zanga a ƙasar Cyprus

Hankula sun tashi a Cyprus,gabannin taron ministocin kuɗi na ƙungiyar Tarayyar Turai, da ake shirin gudanarwa a Brussels da nufin samar da hanyoyin magance matsalar tattalin arziki da ƙasar ta faɗa ciki.

Ɗarurruwan jama'a ne galibi ma'aikata suka gudanar da zanga zanga a babban birni Cyprus, a gaban fadar shugaban ƙasar a daidai lokacin da hukumomin ke ci gaba da tattaunawa domin ceto ƙasar daga durƙushewar tattalin arziki kafin gobe litinin.

Wa'adi na ƙarshe da Babban Bankin Tarayyar Turai ya tabbatarwa ƙasar na ta samar da biliyan 17, ko kuma Bankin ya dakatar da bai wa bankunan ƙasar taimako. Ko da shi ke ministan kuɗi na Cyprus, Micheal Sarris yace, ana samun gagarumin ci-gaba a tattaunawar da ake yi tsakanin su da ƙungiyar Tarrayar Turai da kuma Asusun Ba da Lamuni na Duniya, IMF. Amma har yazuwa yanzu wasu yan ƙasar na ganin ya na da wahala cikin lokaci ƙanƙane a iya shawo kan matsalar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi