1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe mutane 50 a jihar Zamfara

April 6, 2019

Wasu mutane dauke da makamai sun hallaka fararen hula da 'yan kato da gora akalla 50 a wata arangamar da ta auku a garin Kauran Namoda na jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

https://p.dw.com/p/3GOTU
Nigeria Viehdiebstähle in ländlichen Regionen
Nan dai makamai ne da 'yan sandar Najeriya suka kwace daga hannun masu barayin shanu a Gusau babban birnin jihar ZamfaraHoto: DW/Katrin Gänsler

A Tarayyar Najeriya rahotanni daga Arewa maso Yammacin kasar sun tabbatar da mutuwar mutane akalla 50 sakamakon wata mummunar kafsawa da ta auku tsakanin wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton barayin jama'a ne da mayakan sa kai 'yan kato da gora a garin Kauran Namoda da ke ihar Zamfara.

A wata fira da wakilinmu daga jihar Yusuf Ibrahim Jargaba kakakin majalisar dokokin jihar, Alhaji Sanusi Garba ya tabbatar da mutuwar mutanen yana mai cewar masarautar garin Kauran Namoda ce ta dauke su don tabbatar da tsaro a yayin da ya je yiwa masarautar ta'aziyya.

Rahotanni sun ce arangamar ta auku ne a karshen wannan makon a jihar ta Zamfara wacce ke kan gaba daga jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya da ke fama da hare-haren 'yan bindiga kusan kowane mako, tare da salwantar da rayukan al'ummar da ba su san hawa ba su san sauka ba.