1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar rashin tsaro a Jihar Zamfara ta yi kamari

Abdourahamane Hassane
September 1, 2021

A Najeriya gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da rufe makarantun jihar baki daya domin dakile matsalar rashin tsaro da ta yi kamari a jihar.

https://p.dw.com/p/3znEl
Nigeria | Entführung hunderter Mädchen in Zamfara
Hoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Daukar matakin ya biyo bayan satar wasu daliban sama da guda dari a makarantar sakandiren Kaya da ke karamar hukumar Muradun da ke cikin jihar ta  Zamfara da wasu yan bindigar suka yi. Wakilin DW a Katsina ya ce satar daliban na zuwa ne bayan da gwamnatin Jihar ta zamfara ta dauki matakan rufe kasuwannin jihar da hana yawo da babura mutum uku.