1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman sulhu kan rikicin Libiya

Ahmed SalisuJanuary 10, 2015

Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta jagoranci wani sabon zama cikin makon gobe a birnin Geneva don yin sulhu tsakanin bangarorin da ke gaba da juna a Libya.

https://p.dw.com/p/1EIRs
Gefechte in Tripoli Libyen 22.10.2014
Hoto: Reuters/Ismail Zitouny

Manzon musamman ma Majalisar ta Dinkin Duniya Bernardino Leon ya ce tattaunawar na da muhimmancin gaske duba da yadda kasar yanzu ke cikin wani yanayi na rashin tabbas.

Tattaunawar inji Mr. Leon za ta maida hankali ne wajen samar da wani yanayi da zai kawo karshen rikicin da bangarorin ke yi a kasar da samar da gwamnatin hadin kan kasa gami da kaiwa ga samar da sabon kundin tsarin mulki.

Kasashen duniya dai na cigaba da nuna fargabarsu ta dagulewar lamura baki daya a Libya din muddin ba a dauki mataki kan rikicin kasar cikin gaggawa ba.