1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman makokin Fidel Castro a Kuba

November 26, 2016

Hukumomin Kuba sun ayyana makoki na kwanaki tara domin jimamin tsohon shugaban juyin juya hali Fidel Castro, wanda ya yi tasiri cikin siyasar kwamunisanci a shekaru 47 da ya yi ya na mulkin kasar

https://p.dw.com/p/2THpw
Kuba Fidel Castro
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Ernesto

Hukumomin Kuba sun ayyana makoki na kwanaki tara don jimamin tsohon shugaban juyin juya hali Fidel Castro, wanda ya yi tasiri cikin siyasar kwamunisanci a shekaru 47 da ya yi ya na mulkin kasar, kafin rasuwarsa a yammacin wannan Juma'ar da ta gabata.

 

A yanzu haka dai an dakatar da sayar da barasa, kana an sauke tutocin kasar zuwa rabi, daura da soke duk wasu bukukuwan nune-nune, tun bayan da kaninsa kuma shugaba mai ci Raul Castro ya sanar da mutuwar dan uwan nasa, ba tare da bada dalilan sanadiyyar ajalinsa ba. 

 

Ana shirin gudanar da gagarumin gangami a cibiyar juyin juya hali na Havana a birnin Santiago da ke yankin gabashin Kuba, a wani mataki na karrama Fidel Castro, wanda ya mutu ya na da shekaru 90, a ranar Juma'a da dare
 

Shugabannin kasashen duniya na cigaba da aikewa da sakonnin ta'aziyyarsu zuwa ga gwamnati da al'ummar kasar Kuba, dangane da mutuwar tsohon shugaban juyin juya hali wanda ya kafa gwamnatin kwaminisanci, Amurka na ji na gani.

 

Mikhail Gorbachev, shugaban karshe na Tarayyar Soviet, wanda ya kasance mai ba da shawarwari a fannin tattali da siyasar kasar, ya ce Fidel Castro ya bar babban tarihi ba wai ga al'ummar Kuba kadai ba amma har ga duniya baki daya. 

 

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bayyana marigayin da kasancewa abun koyi ga kasashen duniya masu yawa. Nicolas Mandura na Venezuela ya ce Castro ya karfafawa kasarsa gwiwa ta hanyoyi daban daban.