Zaman makoki na kwanaki uku a Turkiya | Labarai | DW | 10.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaman makoki na kwanaki uku a Turkiya

Rahotanni daga kasar Turkiya na nuni da cewa ana kyautata zaton wasu mutane biyu ne suka kai mummunan hari kan masu zanga-zangar lumana a kasar.

Firaministan Turkiya Ahmet Davutoglu

Firaministan Turkiya Ahmet Davutoglu

A wani jawabi da Firaministan kasar Ahmet Davutoglu ya yi ga taron manema labarai, ya yi tir da harin wanda kawo yanzu aka hakikance ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 86 tare kuma da jikkata wasu da dama. Davutoglu ya shaidawa manema labaran a Ankara cewa akwai kwakkwarar alama da ke nuni da cewa mutane biyu ne suka kai harin inda ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki yana mai cewa:

"Mun tattauna da shugaban kasa, dangane da al'ummarmu da suka rasa rayukansu a wannan harin ta'addancin da sojoji da 'yan sanda da kuma fararen hula, bisa alhinin da muke ciki ina mai ayyana kwanaki uku na zaman makoki."

Wannan harin dai na zuwa ne kasa da wata guda gabanin gudanar da zabuka a Turkiyan.