Zaman makoki a Ukraine | Labarai | DW | 15.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaman makoki a Ukraine

Gwamnati ta bukaci da a yi zaman makoki a duk fadin kasar sakamakon harin da ya hallaka wasu 'yan kasa dake balaguro a wata mota kirar bus.

Ana zaman makoki na yini guda a yau Alhamis a fadin kasar Ukraine, sakamakon wani harin da wasu sojoji 'yan awaren Rasha suka kai wanda ya halaka mutane goma sha uku wadanke cikin wata motar Bus.

Shugaban kasar Petro Poroshenko, ya ce tilas ne a girmama wadannan 'yan kasa da miyagu suka halaka a gabashin kasar.

Sai dai a nasu bangaren sojojin awaren na Rasha, sun karyata zargin da aka yi masu, suna mai cewa sojojin Ukraine ne suka kai hari a wani yanki na Volnovaka da nufin murkushe su.

Wasu hotunan na'urorin bincike, sun nunar da mumunar ragargazar da makamin roka ta yiwa motar, da harin ya shafa a ranar Talatar da ta gabata.