Zaman lafiya ba zai samu ba ta hanyar gina matsugunai-Abbas | Labarai | DW | 21.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaman lafiya ba zai samu ba ta hanyar gina matsugunai-Abbas

A wani taron manema labaru na hadin guiwa da suka yi da Barack Obama a Ramallah, Mahmud Abbas ya ce fadada matsugunan Yahudawa na kawo cikas ga shirin zaman lafiya.

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya fada wa shugaban Amirka Barack Obama da ya kai wata gajeriyar ziyara a Gabar Yamma ta Kogin Jordan cewa ba za a samu zaman lafiya da Isra'ila ta hanyar tashe tashen hankula, mamaya da gina matsugunan Yahudawa da kuma kin amincewa da 'yancin 'yan gudun hijira ba. Abbas ya fadi hakan ne a wani taron manema labarai na hadin guiwa da suka yi da shugaba Obama a birnin Ramallah. Kalaman dai na daga cikin jerin korafe korafe da Falasdinawa ke wa Isra'ila. Abbas ya jaddada bukatar kafa wata kasar Falasdinu a Gabar Yammacin Kogin Jordan, Gaza da kuma gabacin Birnin Kudus, yankunan da Isra'ila ta kwace a yakin shekarar 1967, wanda kuma tun a wancan lokaci kasar ta Yahudun Isra'ila ta yi ta gina dubban matsugunan Yahudawa 'yan share wuri zauna. Shi ma a nasa bangaren shugaba Obama ya yi tir da aikin gina unguwannin Yahudawan da Isra'ila ke ci-gaba da yi, abin da ya ce yana kawo cikas ga kokarin samar da zaman lafiya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe