Zaman lafiya a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo | Siyasa | DW | 06.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaman lafiya a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

Duk da nasarar da gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta ayyana a kan 'yan tawayen M23, masu ruwa da tsaki sun ce da sauran aiki tukuna.

Masu ruwa da tsaki a kokarin warware rikicin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, sun bukaci hukumomin kasar su himmatu wajen bin tafarkin siyasa domin kawo karshen rikicin da kasar ke fama dashi baki daya, maimakon dogaro da abin da suka kwatanta da kwarya kwaryar zaman lafiyar da aka samu a yanzu.

Bayan tsawon watanni na gudanar da tataunawa a tsakanin gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da kuma 'yan tawayen M23, a birnin Kampala na kasar Uganda ba tare da cimma wata nasara ba, a yanzu dakarun gwamnatin Kongo sun ayyana samun galaba a kan 'yan tawayen.

A cewar kakakin rundunar sojin kasar ta Kongo dai, mataki na gaba da za su dauka shi ne tabbatar da kwance damarar daukacin kungiyoyin sa kai da ke dauke da makamai, kuma suke taka rawa a rikicin na Kongo, ko dai daga ciki ne ko kuma daga wajen kasar.

GettyImages 178265177 The head of the UN Stabilization Mission in the Democratic Republic of Congo (MONUSCO) and special envoy of the UN secretary-general, Martin Kobler (R), gives a press conference on August 28, 2013 at the headquarters of the UN peacekeeping mission in Kinshasa. UN attack helicopters joined Congolese government troops in an operation on August 28 against rebels in the east of the Democratic Republic of Congo, the UN peacekeeping force said. The operation against M23 rebels in the hills of Kibati north of the regional capital Goma also involved UN and DR Congo army artillery. AFP PHOTO / JUNIOR D. KANNAH (Photo credit should read JUNIOR D.KANNAH/AFP/Getty Images)

Martin Kobler, Manzon Majalisar Dinkin Duniya a Kongo

Majalisar Dinkin Duniya ta yaba da zaman lafiya a Kongo

A martanin da ya mayar dangane da batun, Martin Kobler, manzo na musamman da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya tura zuwa Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, kana jagoran ayyukan Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Kongo, ya ce har yanzu fa da sauran rina a kaba dangane da batun zaman lafiya a Kongo.

Ya ce "Tilas in bayyana cewar, E' na yi amanna da wannan zaman lafiyar. Mun dade muna kokarin ganin ya tabbata, amma yin galaba a kan kungiyar 'yan tawayen M23, na nufin bangaren soji ne kawai, domin a siyasance ba a kai ga kawo karshen rikicin ba tukuna."

Dama dai ana zargin kasar Ruwanda ce da nuna goyon baya ga mayakan kungiyar ta M23 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, zargin da kuma hukumomin kasar suka sha karyatawa. Tunda a yanzu gwamnati ta kai ga yin nasara a kan 'yan tawayen, a cewar Abdulkarim Harerimana, dan majalisar dokokin Ruwanda da ke wakiltar kasar a majalisar dokokin kasashen yankin gabashin Afirka, nasarar, abin farin ciki ne ga daukacin kasashen yankin - ciki harda Ruwanda:

Ya ce "Idan har yanzu M23 ta yanke shawarar daina yakar gwamnatin kasarta, to, abin marhabin lale ne kuma abin farin ciki ne ga Ruwanda a matsayin kasa da kuma al'ummarta. Sai dai kuma muna kara yin kira a garesu da su dauki matakan kawo karshen rikicin baki daya, domin hakan alheri ne a garesu da kuma yankin baki daya."

AUSSCHNITT - bitte nur in klein auf der Seite nutzen und Qualität überprüfen! In this Wednesday Nov. 21, 2012 photo released by Uganda's Presidential Press Services, Uganda's President Yoweri Museveni, left, talks with his counterparts Paul Kagame of Rwanda, right, and Joseph Kabila of Congo during a meeting in Kampala, Uganda. The three heads of the states want the M23 rebels out of Goma, a town they captured from Congo army. (Foto:Presidential Press Services/AP/dapd)

Shugaba Museveni na Uganda (hagu), da shugaba Kagame na Ruwanda

Martanin kasashen yankin gabashin Afirka

Al'ummomin yankin baki daya ne dai ke fatan dorewar zaman lafiya a Kongo, wanda suke ganin zai ta'allaka ne kawai ga irin abubuwan da za su biyo bayan nasarar da hukumomin Kongo suka ayyana a kan 'yan tawayen na M23. Ali Mutasa, dan jarida a kasar Uganda, kana mai sanya ido a kan yadda lamura ke tafiya a yankin, ya ce akwai bukatar gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta daukin matakan tabbatar da dorewar nasarar da ta ce ta samu:

Ya ce " Samun zaman lafiya mai dorewa zai dogara ne kawai a kan aiwatar da tanade tanaden da ke cikin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a birnin Kampala ba tare da tawaya ba - kamar yadda M23 ta bayyana. Idan har gwamnati ta ki yin hakan, to, kuwa M23 za ta sami hujjar sake daukar makamai domin ci gaba da yaki."

Hukumar Kula da 'yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewar, tun bayan barkewar tawayen kungiyar M23 a shekara ta 2012, kimanin mutane dubu 800 ne suka tserewa matsugunansu, yayin da hatta a makonni biyun da suka gabata ma, kimanin mutane dubu 19 ne suka sami mafaka a kasar Uganda da ke makwabtaka da Kongon.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Pinado Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin