Zaman dirshen a filin jirgin sama na Kano | Labarai | DW | 08.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaman dirshen a filin jirgin sama na Kano

Rahotanni daga Kano a Najeriya na cewar matasa na zaman dirshen a filin jirgin saman Kano don ganin an yi cikakken bincike game da jirgin nan mai makamai da ake tsare da shi.

Wakilinmu da ke Kano Nasir Salisu Zango ya ce jami'n tsaro na cigaba da gadin jirgin yayin da a hannu guda ya ce matasan ba sa fuskantar wata barazana daga jami'an na tsaro sakamakon wannan zaman dirshen din da suke yi.

Wannan dai na aukuwa daidai lokacin da jakadan Faransa da ke Najeriya ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatin Najeriyar za ta amincewa jirgin ya bar filin jirgin saman don isa Chadi inda zai sauke kayan wanda za a yi amfani da su wajen yaki da ta'addanci.

To sai da a daura da wannan, jamian tsaron Najeriyar da ke tsare da jirgin sun ce ba za su bari ya tashi ba har sai an kammala gudanar da bincike kamar yadda wata majiya ta rundunar sojin kasar ta shaida.