1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman dar-dar tun bayan juyin mulki

April 18, 2013

A lokacin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya 'yan tawayen Séléka sun yi alkawarin tabbatar da tsaro da zaman lafiya, amma har yanzu ana fama da rigingimu.

https://p.dw.com/p/18IxC
Hoto: AFP/Getty Images

A cikin watan Maris kawancen kungiyar 'yan tawayen Séléka karkashin jagorancin Michel Djotodia suka karbi ragamar mulki a Bangui bayan sun kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasa Francois Bozizé. Sai dai tun daga wannan lokaci kasar ba ta ga zaman lafiya da tsaro ba. Ana ci-gaba da tashe tashen hankula.

A kasa mun yi muka tanadin rahotanni daban daban kan halin da ake ciki a Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya.