Zaman ɗar-ɗar tsakanin Koriya ta Kudu da ta Arewa | Labarai | DW | 01.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaman ɗar-ɗar tsakanin Koriya ta Kudu da ta Arewa

Ana ta ƙara yin ɗamarar yaƙi da shiga shirin ko ta kwana a kan iyakokin Koriya ta Arewa da ta Kudu

epa03644058 A picture released by the North Korean Central News Agency (KCNA) on 29 March 2013 shows North Korean leader Kim Jong-un (sitting) convening an urgent operation meeting at 0:30 am on 29 March 2013 at an undisclosed location, in which he ordered strategic rocket forces to be on standby to strike US and South Korean targets at any time. Kim's order followed two US stealth bombers' first-ever drill over the Korean Peninsula the previous day. The North berated the drill as US hostility against it. EPA/KCNA SOUTH KOREA OUT NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++ / Eingestellt von wa

Shugaban ƙasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un, tare da manyan hafsoshin sojin ƙasa

Shugaba Park Geun-Hye ta Koriya ta Kudu ta ce kasar ta ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen maida martani muddin Koriya ta Arewa ta kai mata hari.

Uwargida Park ta ambata hakan ne a wannan Litinin din bayan da ta gudanar da wani taron gaggawa da manyan jami'an sojin kasar da kuma ministan tsaron kasar Kim Kwan-Jin, biyo bayan shelar da Pyongyang ta yi cewar Koriyoyin biyu na ciki wani yanayi na yaki.

Wadannan kalamai na shugaba Park na zuwa ne daidai lokacin da 'yan majalisar dokokin Koriya ta Arewa wadda ake yi wa kallon 'yan amshin shata ta ke dab da gudanar da wani babban taronta na shekara-shekara wanda zai duba batutuwa da su ka shafi kasar da ma dai dangantaka tsakanainta da Koriya ta Kudu.

Tuni dai kasashen da ke yankin su ka fara yin kiraye-kiraye ga kasashen biyu da su kai zuciya nesa domin gudan fadawa yaki wanda a cewarsu ba zai amfana mu su da mai idanu ba.

Mawallafi: Ahmed Salisu

Edita: Usman Shehu Usman