Zaman ɗarɗar a Kirgistan | Labarai | DW | 18.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaman ɗarɗar a Kirgistan

Yawan waɗanda suka mutu a rikicin ƙabilancin KIrgfistan ka iya zarta wanda aka bayar

default

Sansanin 'yan gudun hijirar da suka tsere daga rikicin Kirgistan

Bisa ƙiyasin gwamnatin riƙon ƙwayar Kirgistan, yawan mutanen da suka rasu a rikicin ƙabilancin ƙasar ka iya ninka adadin da aka bayar har sau 10. Shugabar riƙon ƙwaryar ƙasar Rosa Otunbayewa ta ce rikicin ya rutsa da mutane da yawa a yankunan karkara, waɗanda aka yi saurin binne su bisa al'adar yankin. A hukumance mutane 191 ne aka tabbatar da mutuwarsu kawo yanzu. A halin da ake ciki shugabar tana ziyarar yankin dake kewayen biranen Osh da Jalalabad na kudancin ƙasar a wani mataki na kwantar da hankulan mutane. Wasu alƙalumman da MƊD ta bayar sun yi nuni da cewa mutane aƙalla dubu 400 suka tsere daga rikicin kuma kimanin dubu 100 sun nemi mafaka a maƙwabciyar ƙasar wato Uzbekistan. Wasun 'yan gudun hijirar sun ce an yi musu kisan ƙare dangi. An ƙone gidajensu an kashe 'ya'yansu maza. Har yanzu gawarwakinsu suna nan yashe akan tituna.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammad Abubakar