1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Cika shekaru 50 da dan Adam ya sauka duniyar wata

Mohammad Nasiru Awal AMA
July 30, 2019

Kumbon Apollo 11 da Amirka ta harba 16 ga watan Yuli,1969 a duniyar wata ya yi nasarar sauka da 'yan sama jannati uku a ranar 20 ga watan na Yuli na shekarar wanda hakan ke a matsayin matakin kololuwar gasa ta fasaha tsakanin Tarayyar Sobiet da Amirka. Shirin Taba Ka Lashe ya duba batun.

https://p.dw.com/p/3MxEg

Tun dai a cikin shekaru gommai na 1950 tarihin tafiyar dan Adam zuwa sararin samaniya ya faro. Lokaci ne da aka yi gogayya tsakanin manyan daulolin duniya biyu wato Amirka da Tarayyar Sobiet wajen mallakar makaman nukiliya. A tunaninsu duk wanda ya mallaki sararin samaniya shi zai jagoranci duniya a fannin soji. Hakazalika duk wani kumbon da za a harba sararin samaniya zai iya daukar bama-baman naukiliya. A cikin shekarun 1950 Tarayyar Sobiet na gaban Amirka a binciken sararin samaniya.

A ranar 16 ga watan Yuli, 2019, Amirka ta harba Kumbon Apollo 11, wanda ya yi nasarar sauka a duniyar wata dauke da 'yan sama jannati uku a ranar 20 ga watan na Yuli na shekarar 1969. Neil Armstrong shi ne dan Adam na farko da ya sanya kafarsa kan duniyar wata. Wannan dai ya sa an kai kololuwar wata gagarumar gasa ta fasaha tsakanin Tarayyar Sobiet da Amirka. Shirin na Taba Ka Lashe ya yi waiwaye da Hausawa kan ce shi ne adon tafiya a dangne da tafiye-tafiye da dan Adam zuwa sararin samaniya.