1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

zaben zakaran gwajin dafin dorewar mulki na dimokradiyya a iraqi

December 15, 2005
https://p.dw.com/p/BvGL

Bayanai da suka iso mana daga Iraq na nuni da cewa mutanen da suka cancanci yin zabe a kasar naci gaba da tururuwa izuwa runfunan zabe don kada kuriun su na samar da cikakkiyar gwamnati, bayan kifar da gwamnatin Saddam Hussain.

Rahotannin sun tabbatar da cewa tashe tashen hankulan da aka fuskanta a Bagadaza, bai kawo cikas ba game da fitowar mutanen jefa kuriun nasu.

Ana dai sa ran mutane miliyan goma sha biyar da suka cancanci yin zaben ne zasu kada kuriun nasu don zabar yan majalisun dokoki 275.

Bayanai dai sun nunar da cewa da yawa daga cikin mabiya darikar sunni naci gaba da fitowa don kada kuriun nasu, sabanin kauracewa hakan da suka yi a zaben watan Janairu daya gabata.

Ya zuwa yanzu dai ana hasashen cewa gamayyar jamiyyun darikar shi´a ne zasu lashe wadan nan kujeru da gagarumin rinjaye.