Zaben yan majasa a Maroko | Labarai | DW | 07.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben yan majasa a Maroko

Shugaban jammiyyar Islama da adalci ta PJD dake kasar Moroko ,yayi ikirarin cewa jammiiyar su ce ,zata samu gagarumar nasara a zaben yan majalisa dake gudana a wannan kasa a yau.Dayake hira da manema labaru kafin ya kada kuriarsa tare da mai dakinsa Halima,a harabar makarantar primary dake Sale,Saad Eddie Othmani ,yace zasu lashe wannan zaben babu makawa.Ya hakikance cewar zasuyi gaskiya da adalci,kuma ujammiiyasu ta PJD,itace zata samu mafi yawan kujeru a majalisar Maroko.Mai shekaru 51 kuma likita,Othmani ya jagoranci jammiyyar Islaman tun daga shekaraa ta 2004,inda ya taka rawa wajen gudanar da kamfaign din yaki da cin hanci da rashwa tsakanin masu kada kuriun kasar,batu da manazarta ke ganin jammiiyyar masu sassaucin raayi ta masu hannu da shuni ta gaza,wajen gaggauta yakar talauci a wanna kasa.Manazarta dai sun bayyana cewa,jammiyyar na iya samun nasara a wannan zaben,idan har ta cigaba da kasance,jammiyya daya mafi girma.