Zaben ´yan majalisar dokoki a janhuriyar Azerbaidjan | Labarai | DW | 06.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben ´yan majalisar dokoki a janhuriyar Azerbaidjan

An fara kada kuri´a a zaben ´yan majalisar dokokin kasar Aserbaidjan dake cikin tsohuwar tarayyar Sobiet. Ana ganin zaben a matsayin wani zakaran gwajin dafi ga shirin gwamnati na kafa sahihiyar demukiradiya. Kimanin masu sa ido a zabe dubu daya daga ko-ina cikin duniya ke kula da zaben na Aserbaidjan. A halin da ake ciki sun fara saka ayar tambaya game da sahihancin zaben na yau, bayan rahotannin da aka bayar cewar hukumomi na tursasawa tare da kame magoya bayan ´yan adawa. Kuri´ar jin ra´ayin jama´a da aka gudanar baya bayan nan ta nunar da cewa jam´iyar gwamnatin dake ci ta Ilham Aliyev zata lashe zabe da gagarumin rinjaye.